21 Mayu 2021 - 13:37
Haniyah Ya Sake Aika Wa Jagora Imam Khamenei Wasiƙa Da Kiran A Ɗau Matakin Gaggawa Don Kawo Кarshen Ta’addancin Isra’ila

A wata sabuwar wasiƙa da ya aike wa Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, shugaban ɓangaren siyasa na ƙungiyar gwagwarmayar Musulunci HAMAS, Isma’il Haniyah ya yi kira da a ɗau matakin gaggawa don kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci da wuce gona da iri da ‘Isra’ila’ ta ke yi a kan al’ummar Falasɗinu da kuma wajaje masu tsarki musamman masallacin al-Aƙsah mai alfarma.

ABNA24 : A cikin wasiƙar, Ismail Haniya yayi wa Jagoran ƙarin bayani kan halin da ake ciki a Gaza da sauran yankunan Falasɗinawa don haka sai ya buƙaci da a ɗau matakan da suka dace wajen kawo ƙarshen irin waɗannan ɗanyen aiki da sahyoniyawan suke yi, kamar yadda ya buƙaci da a ɗau matakan gaggawa wajen dakatar da Isra’ilan shirin da take yi na korar Falasɗinawa daga birnin Кudus musamman yankin Sheikh Jarrah lamarin da ya haifar da sabon rikici da yaƙin da Isra’ilan ta ƙaddamar kan al’ummar Gaza.

A ranar 10 ga watan Mayun nan ne dai haramtacciyar ƙasar Isra’ila ta ƙaddamar da hare-haren ta’addanci a kan al’ummar Gazan lamarin da yayi sanadiyyar shahadar aƙalla Falasɗinawa 230 cikinsu yara 65 da mata 39 baya ga sama da mutane 1710 da suka sami raunuka.

A kwanakin baya ma dai Isma’il Haniyan ya aike wa Jagoran wasika yana mai jinjinawa Jagoran da kuma Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan irin gagarumar goyon baya da kuma taimakon da take ba wa al’ummar Falasɗinu da kuma ƙungiyoyin gwagwarmayarsu.

342/